Isa ga babban shafi
US

Ana bin Trump bashin Dala miliyan 650

Jaridar New York Times da ake bugata a kasar Amurka ta jiyo cewa ana bin bashin  kamfanonin dan takaran shugabancin kasar karkashin jam'iyar Republican Donald Trump bashin kudade da suka kai Dalan Amurka miliyan 650.

Dan takaran shugabancin Amurka karkashin jamiyyar Republican Donald Trump
Dan takaran shugabancin Amurka karkashin jamiyyar Republican Donald Trump REUTERS/Eric Thayer
Talla

Cikin sabuwar jaridar da ta fito a yau Asabar ta ce yawan bashin ya saba da bayanai da dan takaran ya gabatar gameda irin basuka dake wuyansa.

Jaridar ta wakilta wani kamfani ne mai zaman kansa dake harkan tattara bayanai na kaddarori da mutane suka mallaka domin gano mata basukan dake wuyan dan takaran.

Bayaga wadannan basuka, bincike ya nuna Donald Trump na da jari cikin wasu kamfanoni da ake bi bashi na kudin Amurka Dala Biliyan biyu.

Donald Trump ya fadi a wajen wani taro a yakin neman zabe da yake yi cewa ya mallaki kaddarori da suka kai na kudin Amurka Dala Biliyan 10.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.