Isa ga babban shafi
Philippines

Duterte ya gargadi Majalisar dinkin Duniya

Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte ya gargadi Majalisar Dinkin Duniya da kakkausan harshe game da sukar matakin gwamnatinsa na kisan masu safara da kuma tu’ammali da miyagun kwayoyi a kasar.

Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte
Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte
Talla

A cewarsa yawan masu laifin da ya bada umurnin kashewa bai taka kara ya karya ba.

Duterte wanda ya tun bayan zamansa shugaban kasar Philippines ya yi alkawarin magance safarar miyagun kwayoyi a kasar, yace zai cigaba da awaitar da manufar gwamnatinsa duk da kokawar majalisar dinkin duniya.

Lokacin da yake jawabi yayin bikin cika shekaru 115 da kafuwar rundunar ‘Yan sandan kasar, Duterte ya ce bai ga dalilin da zai sa Majalisar dinkin Duniya ta damu da kashe miyagu Dubu daya kacal ba, kamar yadda ya fada.

A satin da ya gabata ne sashin yaki da safarar miyagun kwayoyi na Majalisar dinkin Duniya ya bayyana damuwa bisa yawan masu tu’ammuli da kwayoyi da ake kashewa a kasar ta Philipinnes.

Sai dai a bangarensa shugaba Duterte ya ce baya son ganin wata tawagar masu sa ido kan hakkin dan’adam daga majalisar dinkin duniya cikin kasar don kuwa ba a maraba da su.

Duterte dai ya bawa “yan sandan kasar dama kungiyoyin fararen hula umurnin kashe duk wani mai tu’ammali da miyagun kwayoyi, da suka kama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.