Isa ga babban shafi
Philippines

An rantsar da Duterte a Philippines

An rantsar da Rodrigo Duterte a matsayin shugaban kasar Philippines na 16, a wani takaitaccen biki da aka yi a fadar shugaban kasar, sabanin yadda aka saba yi don kaucewa kashe kudin jama’a.

Rodrigo Duterte na Philippines.
Rodrigo Duterte na Philippines. Reuters
Talla

Shugaban ya sake jaddada matsayinsa na kashe masu aikata manyan laifufuka da kuma yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Rodrigo Duterte ya sake jaddada aniyarsa na kashe dubban masu aikata manyan laifufuka a kasar a mulkin sa na shekaru 6, yace babu wani shugaba da zai samu nasarar mulki ba tare da hadin kan al’ummar kasa ba.

Shugaban yace zai dawo da aiwatar da hukuncin kisa da kuma ba ‘Yan Sanda izini harbe masu safarar kwayoyi.

Dan shekaru 71, Duterte ya zama shugaban kasa mafi yawan shekaru a Yankin kudancin Asia, a kasar da ke dauke da mutane sama da miliyan 100.

An dai zarge shi da mallakar kungiyar ‘yan banga wadda ta kashe mutane sama da 1,000 a Yankin Davao inda ya rike mukamin Magajin Gari.

Shugaban y ayi alkawarin bada umurnin birne gawar tsohon shugaban kasa Ferdinand Marcos a makabartar shahararun mutanen kasar dan hada kan al’ummar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.