Isa ga babban shafi
china

China nada damar samar da tsaro a tekun Sin

Wani babban jami’in gwamnatin China ya bayyana cewa kasar nada damar samar da tsaro ta sama a tsibirin da kasar ke takardama akai da Philippines wanda ke kudacin tekun Sin.

Tsibirin da ake takardama akai tsakanin China da Philippines
Tsibirin da ake takardama akai tsakanin China da Philippines Reuters/路透社
Talla

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Liu Zhenmin ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar kwana guda bayan kotun duniya ta yanke hukuncin cewa, China ba ta da hurumin mallakar tsibirin.

Kasar Philippines ce ta shigar da kokenta a gaban kotun wadda ke  birnin Hague kuma dukkanin kasashen biyu sun sanya hannu domin amincewa da kafa kotun a karkashin majalisar dinkin duniya.

Shugaban China Xi Jinping ya ce, wannan hukucin ba zai haramta wa China damar gudanar da harkokinta kan teken ba.

Shi kuwa jakadan China a Amurka, Cui Tiankai cewa ya yi, matakin da kotun ta dauka zai dada jefa yankin cikin rikici kuma hakan zai zama karan tsaye ga dokokin duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.