Kotu ta ba China rashin gaskiya akan Phillippines
Wata kotun duniya a Hague ta zartar da hukuncin da ya ba China rashin gaskiya kan takaddamar da kasar ke yi da Philippines na mallakar wani tsibiri da ke kan teku a kudancin China.
Wallafawa ranar:
A yayin da kotun ke yanke hukuncin ta ce China ta sabawa ‘yancin kasar Philippines akan mamayar yankin da ta ke yi.
A yau Talata ne kotun ta yanke hukuncin kan takaddamar game da mallakar tsibiran da ke kan teku a kudancin kasar China.
Kasar China ta ki halartar zaman kotun tare da yin watsi da hukuncin da kotun ta zartar a yau kamar yadda ta fitar da sanarwa bayan yanke hukuncin.
China ta ce ba a bata damar kare kanta ba a kotun kan ikirarin da ta ke na mallakar yankin tsibiran mai arziki.
Kasar Philippines ce ta gabatar da koken a gaban kotun ta Hague wacce kasashen biyu suka sanya hannun amincewa da kafa kotun a karkashin Majalisar Dinkin Duniya.
Tuni gwamnatin Philippines ta gargadi ‘yan kasarta da ke China da su yi taka-tsan-tsan don kaucewa duk wata barazana da kan iya tasowa bayan yanke hukuncin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu