An kama wadanda suka kitsa harin Madina
Hukumomin Saudiya sun cafke mutane 19 da ake zargi da hannu a hare-haren ta’addancin da aka kai wa kasar a ranar Litinin da suka hada da wanda aka kai kusa da masallacin Annabi da ke birnin Madina.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
An kama mutane 12 ‘yan asalin kasar Pakistan da kuma mutane 7 ‘yan asalin kasar ta Saudiya yayin da aka bayyana wani matashi mai shakaru 26 a matsayin wanda ya kai harin Madina.
Matashin mai suna Naer Muslim Hamad, dan asalin Saudiya ne kuma rahotanni sun ce, mai mu’amala da miyagun kwayoyi ne.
Harin na Madina shi yafi tayar da hankulan kasashen musulmi na duniya, lura da matsayin birnin wanda ke dauke da kabarin Annabi Muhammadu tsira da amincin Alla su kara tabbata a gare shi.
Masharta dai na ganin cewa kungiyar IS mai da’awar kafa daular Islama, ita ce ta shirya hare haren da aka kai Madina da Jedda da kuma Qatif duk a rana guda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu