Isa ga babban shafi
Saudiya

Bom ya tashi a kusa da Masallacin Annabi a Madina

An kai harin kunar bakin wake a kusa da Masallacin Annabi SAW a Madina, wanda shi ne hari na uku da aka kai a kasar a ranar Litinin bayan harin da aka kai a Masallacin Shi’a a garin Qatif da kuma ofishin jekadancin Amurka a Jidda.

Bom ya tashi a Masallacin Annabi na Medina
Bom ya tashi a Masallacin Annabi na Medina REUTERS
Talla

An kai harin ne lokacin da ake shirin Sallar Magariba.

Kafar Yada labarai ta Saudi Gazzete ta nuna hoton bidiyon wata mota na cin wuta a kusa da harabar Masallacin Madina inda Kabarin Manzon Allah SAW ya ke.

Wasu rahotanni na cewa mutane akalla hudu suka mutu.

Tashin bom din zuwa ne bayan wani dan kunar bakin wake ya tarwatse kan shi a harabar Masallacin mabiya Shi’a a garin Qatif da ke gabashin Saudiya bayan harin farko da aka kai a ofishin jekadancin Amurka a yau Litinin.

Babu dai wata kungiya ta da fito ta yi ikirarin kai hare haren a yayin da ake kwanakin karshe na kammala Azumin Ramadan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.