Isa ga babban shafi
Saudiyya-Amurka

Dan kunar bakin wake ya kashe kansa kusa da ofishin Amurka da ke Jedda

A kasar Saudiyya wani dan kunar bakin wake ya hallaka kan sa dab da ofishin jakadancin Amurka dake Jedda yau Littini.

Sakataren Waje na Amurka John Kerry yayin wata ziyara Saudiyya tare da Sarki Salman
Sakataren Waje na Amurka John Kerry yayin wata ziyara Saudiyya tare da Sarki Salman rfi
Talla

Jami'an tsaro sun gano take-taken mutumin a lokacin da yake yawo a harabar da aka killace don masu ajiyan motoci a Asibitin Dr Suleiman Faqeeh wanda yake kusa da ofishin jadancin Amurka.

Bayanai na nuna mutumin tarwatsa kan sa yayi a lokacin da yaga jami'an tsaro sun tunkare shi.

Jami'an tsaron biyu ne suka sami rauni.

Ma'aikatar Harkokin cikin gida na Saudiyya na kokarin garo tarihin mamacin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.