Obama na fatan dawo da dangantakarsu da Saudiya
Shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya kai ziyara Saudiya, inda ake fatan zai yi amfani da wannan damar wajen warware ban-bancin ra’ayin dake akwai tsakanin kasashen biyu da kuma batun yaki da ayyukan ta’addanci.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A ziyarar ta shi ta kwananki biyu, Mista Obama zai tattauna da hukumomin kasar kan batun kawo karshen yaki a kasahen Syria da Yemen.
Danganta tsakanin Amurka da Saudiya ya yi tsami a ‘yan wannan lokutan, kan batun da Saudiya ke yi cewa Amurkan ba ta mara mata baya kan Iran.
Sai dai ana saran Ziyarar na wannan lokaci ya dai-daita kasashen biyu, Kana a gobe alhamis Shugaba Obama zai halarci taron kasashen larabawan yankin Gulf shida.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu