Isa ga babban shafi
saudiya

Saudiya za ta mayar da martani kan harin Madina

Sarki Salman bin Abdul Aziz na Saudiya ya yi alkawarin mayar da martani kan jerin harin hare-haren ta’addancin da aka kai wa kasar a ranar Litinin din data gabata, cikinsu har da wanda aka kai kusa da masallacin Annabi da ke Madina.

Harin kunar bakin wake kusa da masallacin Annabi da ke Madina a Saudiya
Harin kunar bakin wake kusa da masallacin Annabi da ke Madina a Saudiya REUTERS/Handout EDITORIAL USE ONLY.
Talla

Sarki Salman ya bayyana haka ne a lokacin da yake yi wa al’ummar kasar jawabi kan bikin Eidil Fitr.

Akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu a harin kunar bakin waken na Madina yayin da aka kai wasu hare-haren a masallacin Shi’a da ke garin Qatif da kuma Ofishin jakadancin cin Amuruka a birnin Jedda.

Shugabannin kasashen musulmi na duniya na ci gaba da bayyana damuwa kan harin musamman na masallacin Madina, ganin cewa nan ne mafi daraja ta biyu ga musulman duniya.

Majalisar malamai ta Saudiya da gwamnatocin kasashen Iraqi da Lebanon da Turkiya da Masar duk sun yi tir da harin na wanda suka bayyana a matsayin wuce-gona da iri.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.