Ba mu da niyyar janyewa Rasha takukumai-G7
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce kasashe 7 masu karfin tattalin arziki a duniya ba su da niyyar janyewa takunkuman da suka kakaba wa kasar Rasha a lokacin wannan taro nasu.
Wallafawa ranar:
Merkel ta ce batun cire wa kasar takunkumai sakamakon rawar da take takawa domin wargaza kasar Ukraine wadda babbar aminiya ce ga kasashen 7, sam ba ya cikin abubuwan da suke tattaunawa a kai.
Takukuman karayar tattalin arziki da aka kakkabawa Rasha na cigaba da tasiri ga cigaban tattalin arzikin kasar.
A ranar Alhamis ne Shugaban Kungiyar kasashen Turai Donald Tusk ke bayyana ra'ayinsa kan wannan batu, da yake gani lokaci yayi da za a dai-dai al'amura tsakanin Rasha da Ukraine da kuma batun rikicin tekun kasar China.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu