Isa ga babban shafi
Jamus

An karfafa matakan tsaro a Jamus saboda taron G7

Hukumomin Jamus sun karfafa matakan tsaro a a birnin Elmau dake kudanci kasar, inda za a gudanar da taron kasashe masu karfin tattali arziki a Duniya da ake kira G7

Manyan kasashen duniya na tattaunawa
Manyan kasashen duniya na tattaunawa © AFP
Talla

Ranar lahadi za a soma babban taron kasashen na duniya yayin daJamus mai masauki baki ta girke kusan jami’an tsaro 22.300 a yankin na Elmau.

Taron da zai samu halartar Shugabanin kasasahe kama daga turai dama wasu daga Nahiyar Afrika zai yi dubi ne kan wasu daga cikin matsallolin dake addabar duniya.

Akwai batun rikicin Ukraine, da ake sa ran mahalart taron za su yi nazari a kai tare da bullo da hanyoyin magance matsallar bakin haure dake cigaba da mutuwa a kan hanyar su ta zuwa Turai.

A daoyan bangaren, wasu kungiyoyin a kasar ta Jamus sun bayana damuwar su tare da nuna adawa dangane da wanan taro da suka danganta da taron da ya sabawa dokokin da aka shata a Majalisar dinkin duniya.

Rahotani sun nuna cewa sama da mutane dubu 40 ne suka yi dandazo a birni Munich domin bayana bacin ran su a kai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.