Isa ga babban shafi
Libya

IS ta kashe dakarun Libya 32

Mayakan IS da ke da’awar Jihadi sun kashe dakarun amintacciyar gwamnatin kasar Libya akalla 32 a ci gaba da fada tsakanin bangarorin biyu a kusa da birnin Sirte.

Tun kawar da gwamnatin Ghaddafi Libya ta fada cikin rikici
Tun kawar da gwamnatin Ghaddafi Libya ta fada cikin rikici REUTERS/Asmaa Waguih
Talla

Wani jami’in gwamnati da bai yarda a ambaci sunansa ba, ya ce wasu daga cikin sojojin an harbe su da bindiga ne yayin aka hallaka wasu ta hanyar yin amfani da wata mota da aka dana wa bam.

Gwamnatin Libya ta ce kimanin wasu 50 suka jikkata.

Tuni dai gwamnatin hadin kan ta Libya ta nemi taimakon jiragen yaki domin kaddamar da hare hare akan mayakan IS.

A taron da aka gudanar da Vienna kasashen Amurka da Italiya sun amince da bukatar ta Libya domin tunkarar barazanar IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.