Isa ga babban shafi
Amurka

Ana zaben fid da gwani a Indiana ta Amurka

An fara gudanar da zaben fid da gwani a jihar Indiana ta kasar Amurka, inda Donald Trump na jam’iyyar Republican da Hillary Clinton ta jam’iyyar Democrat ke neman nasarar samun tikitin tsayawa takarar zaben shugabancin kasar mai zuwa.

Hillary Clinton ta Democrat da Donald Trump na Republican
Hillary Clinton ta Democrat da Donald Trump na Republican REUTERS/David Becker/Nancy Wiechec/Files
Talla

Trump dai na fatan magoya bayansa na Indiana za su yi waje da abokan hamayyarsa na Republican yayin da Clinton ke neman karfafa matsayinta domin samun nasarar wakiltan Democrat a zaben shugaban kasar.

An dai bude rumfunan zaben ne da misalin karfe 6 na safe agogon jihar ta Indiana, yayin da jama’a suka isa domin kada kuri'unsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.