Isa ga babban shafi
Amurka

Obama na nan kan bakarsa na rufe Guantanamo

Shugaban Amurka Barack Obama ya sanar da wani tsari da zai ci dala milyan 290 zuwa 475 domin rufe gidan yarin Guantanamo wanda kasar ta kafa kimanin shekaru 14 da suka gabata.

Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama AFP/AFP
Talla

Obama ya ce akwai wasu gidajen yari guda 13 a cikin kasar inda ya ke fatan mayar da fursunoni 91 da suka rage a gidan yarin da aka kafa bayan harin 11 ga watan Satumba.

A cikin jawabinsa, Mista Obama ya gaji matakin rufe gidan yarin ne daga tsohon shugaba Goerge Bush wanda ya kafa gidan yarin kuma ya kudurta rufewa kafin wa’adinsa ya kawo karshe.

Shugaba Obama ya ce yanzu lokaci ya yi da za a rufe gidan yarin domin ba ya son wanda zai gaje shi ya fuskanci kalubalen da ya fuskanta kan gidan yarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.