Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta sasanta rikicin Isra'ila da Falasdinu

Gwamnatin kasar Faransa ta bayyana sabuwar aniyar sasanta rikici tsakanin Isara’ila da Falasdinu tare da fadin cewa za ta amince da Falasdinu a matsayin cikakkiyar kasa matukar kokarin sasantawar ya gaza cimma gaci .

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande da ministan harkokin wajen kasar Laurent Fabius
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande da ministan harkokin wajen kasar Laurent Fabius REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya ce, nan da makwanni masu zuwa Faransa za ta mayar da hanakali wajen shirya taron kasa da kasa a birnin Paris da zai hada bangarorin biyu da kuma aminansu daga Amurka da Turai da yankin Larabawa domin ganin an sasanta tsakanin Isra’ila da Falasdinu.

Tuni dai hukumomin Falasdinu suka yaba da wannan matakin, inda suka ce za su tuntubi Faransa nan da kankanin lokaci.

To sai dai jaridar kasar Isra’la mai suna Haaretz ta rawaito cewa wani babban jami’in kasar ya yi watsi da gargadin da Faransa ta yi na cewa za ta amince da Falasdinu a matsayin cikakkiyar kasa idan sasantawar ta gaza cimma nasara.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.