‘Yan adawa za su kauracewa taron Syria a Geneva
Kungiyar ‘Yan adawar Syria ta jaddada matsayinta na kauracewa taron sasanta rikicin kasar da Majalisar Dinkin Duniya ta sanar za a soma a yau Juma’a a Geneva.
Wallafawa ranar:
‘Yan adawar sun ce za su kauracewa zaman taron har sai an amince da bukatunsu na shigar da kayan jin-kai a yankunan da ke cikin matsananci hali na yunwa.
‘Yan adawar wadanda Saudiya ke marawa baya sun ce sai idan an cim ma yarjejeniyar shigar kayan jin kai sannan za su halarci taron sasanta rikicin na Syria.
Matakin kauracewa taron na ‘Yan adawar ya haifar da fargaba akan nasarar kokarin kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru 5 ana fafatawa a Syria.
Sama da mutane 260,000 suka mutu a rikicin Syria, kuma jekadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Steffan de Mistura yana ganin wannan dama ce ta kawo karshe zubar da jini a kasar.
‘Yan adawar na son dakarun gwamnatin Bashar Al Assad su dakatar kai hari tare da bayar da izinin shigar da kayan jinkai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu