Isa ga babban shafi
Syria

MDD ta yi gargadi akan mutanen Madaya a Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar mutane da dama za su mutu a kasar Syria muddin ba a cire kawanyar da sojoji da yan tawaye suka yi wa wasu yankunan kasar ba da ake fama da yunwa.

Mutanen Madaya na cikin mawuyacin hali a Syria
Mutanen Madaya na cikin mawuyacin hali a Syria REUTERS
Talla

Babban jami’in da ke kula da jinkai a kasar Yakoub El Hillo ne ya yi wannan gargadin.

Gargadin kuma na zuwa ne kwana guda bayan fara kai kayan agaji ga dubban mutanen da suka tagayyara a garuruwan Madaya da Fuaa da Kafaaya.

A garin Madaya wanda sojojin gwamnati suka kewaye , jami’in yace mutane 28 suka mutu sakamakon tsananin yunwa, sannan ya ga yara kanana da suka zama Kaman gwarangwal saboda matsanancin hali na rashin abinci.

Yacoub El Hillo ya bukaci Majalisar Dinkin duniya ta dauki mataki domin kawo karshen kawanyar da yace ta jefa fararen hula cikin halin kakanikayi.

Majalisar Dinkin Duniya tace tana kokarin samar da kayan abinci ga mutane miliyan hudu da rabi a Syria wadanda ke zama a yankunan da ke da wahalar isa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.