Isa ga babban shafi
Syria

Rikicin Saudiya da Iran ba zai shafi Syria ba- MDD

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a kasar Syria Staffan de Mistura yace rikicin da ake yi tsakanin Saudi Arabiya da Iran ba zai shafi yunkurin samar da zaman lafiya a kasar Syria ba.

Yankin Douma, gabashin Ghouta da gwamnatin Syria ta tarwatsa da jiragen yaki
Yankin Douma, gabashin Ghouta da gwamnatin Syria ta tarwatsa da jiragen yaki REUTERS
Talla

Mistura wanda ya ke Magana bayan ganawa da hukumomin Iran ya ce ganawar da ya yi da kasashen biyu ya tabbatar da bukatarsu na ganin an ci gaba da yunkurin samar da zaman lafiya a Syria.

Kasashen biyu na taka rawa sosai a kokarin da ake wajen kawo karshen rikicin Syria wanda ya lakume rayukan dubban mutane tare da tursasawa miliyoya ficewa kasar.

Saudiya ta yanke hulda da Iran bayan kona ofishin jekadancinta a Tehran sakamakon zartar da hukuncin kisa da Saduiya ta yi akan wani malamin Shi’a Nimr al Nimr.

Yanzu haka kuma kasashe da dama aminnan Saudiya sun yanke hulda da Iran, lamarin da masharhanta ke ganin na iya haifar da matsala a kokarin da ake yin a sasanta rikicin kasashen Syria da Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.