Isa ga babban shafi
Saudiya

ISIS ta yi barazanar kai hari a Saudiya

Kungiyar ISIS ta yi barazanar fasa gidajen yarin Saudiya inda ake tsare da mayakanta bayan mahukutan kasar sun zartar da hukuncin kisa akan mutane sama da 40 da suka hada da mayakan Al Qaeda.

ISIS ta yi barazanar kaddamar da hari a Saudiya.
ISIS ta yi barazanar kaddamar da hari a Saudiya.
Talla

Bayan daukar alhakin harin da aka taba kai wa Saudiya, Kungiyar ISIS ta ce, za ta abka wa kasar domin fasa gidajen yarin Al Hair da Tarfiya inda ake tsare da yawancin mayakanta.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta wallafa a intanet ta ce, kubutar da fursunoninta ba zai yiwu ba sai idan ta kawar da mulkin kama karya.

A watan Yuli ne dai wani dan ISIS ya kashe kansa a harin kunar bakin wake a Riyadh, babban birnin Saudiya.

Duk da sabanin da ke tsakaninsu amma Ra’ayin ISIS da Alwada ya zo guda akan adawa da manufofin saudiya da ta dauke su kungiyoyin ‘yan ta’adda tare da kame mayakansu da dama.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.