Saudiya ta kulla kawance da kasashe 34 kan yaki da ta’addanci
Kasar Saudiyya ta kafa rundunar hadin guiwa da ta kunshi kasashe 34 domin yakar ta’adanci da ake fakewa da jihadi ana salwantar da rayukan jama’a.
Wallafawa ranar:
Kasashen da Saudiya ta kulla kawancen da su sun hada da Masar da Turkiya da wasu kasashen a gabas ta tsakiya da Asiya da Afrika.
Amma babu Iran cikin kasashen da Saudiya ta kulla kawancen da su kan yakar Ta’addanci.
Ministan Tsaro na Saudiyya Yarima Mohammed Bin Salman Al-Saud ya ce kawancen kasashen zai tunkari matsalolin kasashen musulmi da ta’addanci.
Sannan za su hada kai da sauran kasashe da ke yaki da ta’adanci a duniya.
Saudiya tace kasashen za su yaki ta’addanci a ko ina a duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu