Isa ga babban shafi
Syria-Saudiya

Saudiya na taron samar da zaman lafiya a Syria

A fara taron nazarin duba yiwuwar sasanta rikicin Syria da ‘yan adawa kasar ke halarta a birnin Riyadh na kasar Saudiya. Wannan dai na zuwa ne gabanni ganawa da ake shirin yi na Musamman da Shugaban Bashar al-Assad.

Talla

Taron na saudiya na zuwa ne, a dai-dai lokacin da kasashen duniya ke duba hanyar dawo da zaman lafiya a kasar Syria

Wannan dai ya kasance karo na farko da ake gudanar da irin wannan taro, duk da dai a baya ansha bukatar yin haka wanda bai samu ba, sai a wannan lokaci.

Ana dai gani cewa akwai bukatar ‘yan adawa Syria sun yi magana da muryar guda tare da gabatar da batutuwan samawa kasar makoma mai kyau.

Shugabanni duniya masu karfin fada aji, a baya sun gana a birnin Vienna inda suka cimma matsaya na kaddamar da shirin tattaunawa zaman lafiyar kasar a siyasance, sai dai sun gagara samun dai-daituwa da Shugaba Bashar al-assad na Syria sakamkon sharudan da suke bukatar ya yi na’am da su.

‘Yan adawa Syria da wasu shugabani duniya na cigaba da daurawa Shugaba Assad alhakin halin da kasar ta fada a ciki na Yaki, inda suke gani cewa babu wata mafita sama da barin Assad kujera Mulki.

Ana dai saran taron na tsawon kwanki Uku, ya taka rawar gani, lura da halin da Syria ke sake fadawa a ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.