Isa ga babban shafi
Saudiya

Mata 17 sun lashe zabe a Saudiya

Akalla Mata 17 ne suka yi nasara a zaben farko a tarihin kasar Saudiya da ya kunshi Mata ‘Yan takara da masu jefa kuri’a da aka gudanar a ranar Assabar.

Wannan ne karon farko da aka dama da Mata a harakokin Siyasar Saudiya
Wannan ne karon farko da aka dama da Mata a harakokin Siyasar Saudiya REUTERS
Talla

Akwai Mata 4 da suka samu nasara a zaben na kansiloli a yankin Jedda, da wata guda a yankin Makkah, da kuma wasu da suka yi nasara a yankunan Qatif da Tabuk da Ahsaa.

Hakan dai na nuna matan sun samu kasa da kashi guda na yawan kujeru 2,106 bayan samun nasarar 17.

Mata 900 ne suka tsaya takara a zaben cikin ‘Yan takara 6,440.

Mata ‘Yan takarar zaben dai a Saudiya sun fuskanci kalubale musamman a wajen yakin neman zabe saboda Karkashin dokokin kasar Matan ba su da ‘yancin yin gogayya da maza ko kuma wallafa hoto domin a zabe su.

Amma Rahotanni sun ce Mata sama da kashi 80 suka fito domin kada kuri’a a zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.