Yankunan da ke fama da yunwa a Syria za su fara samun tallafi
Ana sa ran isar da tallafi zuwa garuruwa uku da ke fama da yunwa a kasar Syria bayan sun kwashe watanni shida ba tare da samun abinci ba sakamakon kawanyar da sojoji suka mu su.
Wallafawa ranar:
Garuruwan sun hada da Madaya da Fuaa da Kafraya.
Mai Magana da yawun Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya Idlin Etefa Abeer ya ce yanzu haka motocin agaji na shirin tafiya garuruwan da aka yi wa kawanya .
A cewar shi yanzu haka an loda kayan abincin a cikin motocin wanda zai kai ga mutane 40,000 da ke Madaya da wasu mutane 20,000 da ke sauran garuruwan biyu.
Ya ce suna fatar cewar gobe kayan abincin za su isa garuruwan, kuma sun tattauna da bangarorin da abin ya shafa don tabbatar da cewar kayan abincin sun isa gare su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu