Isa ga babban shafi
Syria

A rusa Asibitoci 177 a Syria

Kungiyoyin bayar da agaji a kasar Syria sun bayyana, cewa manyan asibitoci 177 ne aka rusa a yakin da ake yi a kasar tare da kashe jami’an asibitoci 700.

An kashe jami’an lafiya 700 a Syria
An kashe jami’an lafiya 700 a Syria REUTERS/Khalil Ashawi
Talla

Kungiyoyin sun bayyana cewa an rusa adadin asibitocin ne tun farkon soma yakin a 2011 zuwa yanzu.

Shugaban hadin guiwar kungiyoyin masu zaman kansu da ke aikin agaji ga asibitocin kasar ta Syria Oubaïda al-Moufti ya ce tun farkon shekara ta 2012 gwamnati da sauran mayaka a kasar suka mayar da kai hare harensu a kan gine ginen kiyon lafiya.

Kungiyar likitocin kasar da ke zaune a kasashen ketare l'UOSSM na aikin kai dauki ne a yankunan da ke rike ga ‘yan tawayen inda suke kai agaji ga mayakan.

A lokacin wani taron manema labarai da kungiyar ta UOSSM ta kira a ranar Laraba a birnin Paris al-Moufti, yace daga 2012 zuwa karshen 2015 sassan kiyon lafiya 330 da suka hada da manyan asibitoci 177 aka ruguza a hare haren na sojojin shugaba Bashar al Assad da ‘Yan tawaye suka kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.