Isa ga babban shafi
Iran

Iran za ta saye jirage 114 kirar Airbus

Kasar Iran ta ce zata saye jiragen Fasinja kimanin 114 kirar airbus, a wani matakin farko na kulla ciniki da kasashe yammaci bayan janye ma ta takunkumin kariyar tattalin arziki.

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani REUTERS/President.ir/Handout
Talla

A cikin makon nan ne Iran za ta sanya hannu kan cinikin jiragen a ziyarar da shugaban kasar Hassan Rouhani zai kai a kasashen Italiya da Faransa.

Ministan sufuri na kasar, Abbas Akhoundi ya bayyana cewa za a kulla yarjejeniyar sayen jiragen a cikin wannan makon nan a Paris

Iran zata saye jiragen ne domin karfafa zirga zirgar jiragenta, abin da ake kallo a matsayin babbar harkar kasuwanci ta farko da kasar ta sanar tun bayan da kasashen duniya suka janye takunkuman da suka kakaba mata saboda shirinta na Nukliya.

Tuni dai shugaba Rouhani ya yaba da matakin janye takunkuman, wanda ya ce ya bude sabon babi ga Iran, lura da cewa yanzu tattalin zrikinta zai koma fagen kasuwannin duniya.

A bangare guda Ministan sufurin ya ce, cikin jiragen sama 250 da Iran ta mallaka, 150 ne kadai ke aiki, yayin da ta kwashe sama da watanni 10 tana kokarin sayen wasu jiragen amma hakan ya ci-tura saboda takunkuman tattalin arzikin da ta ke fama da su.

A cewar ministan, ayarin farko na jiragen zai isa Iran a ranar 19 ga watan Maris, sai dai ba a fadi addadin kudaden da gwamnatin kasar ta kulla yarjejeniya da kamfanin Airbus ba mai kera jiragen sama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.