Isa ga babban shafi
Iran

OIC ta soki Iran kan harin ofishin Saudiya a Tehran

Shugaban kungiyar kasashen musulmi ta Duniya OIC, Iyad Madani, ya ce tsamin dangantaka tsakanin Iran da Saudi Arabiya ba zai haifar da komai ba illa koma baya ga kalubalen da ke fuskantar Musulmi a fadin Duniya.

Masu Zanga-zanga sun kona ofishin jekadancin Saudiya saboda kisan Nimr al Nimr
Masu Zanga-zanga sun kona ofishin jekadancin Saudiya saboda kisan Nimr al Nimr
Talla

Madani ya fadi han ne yayin da ya ke jawabi a taron da Saudiya ta kira na mambobin kungiyar kasashen musulmi 57 bayan masu zanga-zanga sun kona ofishin jekadancinta a Tehran, sakamakon zartar da hukuncin kisa akan malamin Shi’a Nimr al Nimr.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar musulmin ta yi allawai da harin da aka kai wa ofishin Saudiya a Iran.

Sannan kungiyar ta bukaci Iran ta daina shiga harakokin cikin gidan kasashen Larabawa.

Tuni dai wasu kasashen larabawa aminnan Saudiya suka yanke hulda da Iran kan rikicinta da Saudiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.