Isa ga babban shafi
Faransa

Ministocin tsaron kasashe na ganawa kan ISIS

Yau ministocin tsaron kasashe 7 da ke yaki da kungiyar ISIS a kasashen Iraqi da Syria zasu gana a birnin Paris domin nazarin halin da ake ciki da kuma yadda za su karfafa rundunonin da ke yakin.

Ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian.
Ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian. REUTERS/Delmi Alvarez
Talla

Ministan tsaron Faransa Jean Yves Le Drian da takwaransa na Amurka Ash Carter za su jagoranci taron wanda zai samu halartar ministocin Australia da Birtaniya da Holland da Jamus da kuma Italia.

Babu tabbacin halartar Russia wadda ita ma ta kaddamar da harin sama kan mayakan, duk da zargin da kasashen yammacin duniya ke mata cewar tana kai hari ne kan masu adawa da shugaba Bashar al Assad.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.