Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Faransa ta ce ana ci gaba da neman maharan Burkina Faso

Gwamnatin Fasransa ta bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da neman sauran mutane uku da ake zargi da hannu a harin ta’addancin da kungiyar al-Qaeda reshen Magrib ta kaddamar kan wani Otel da ke birnin Ouagadougou na Burkina Faso, inda mutane 30 suka rasa rayukansu.

Otel din Four Star splendid da aka kaddamar da harin ta'addanci a birnin Ouagadougou na Burkina Faso
Otel din Four Star splendid da aka kaddamar da harin ta'addanci a birnin Ouagadougou na Burkina Faso REUTERS/Joe Penney
Talla

Firaministan Faransa, Manuel Vall ya bayyana wa majalisar dokokin kasarsa cewa, an kashe uku daga cikin maharan 6 kuma ana ci gaba da kokarin neman sauran ukun.

Jami’an tsaron Burkina Faso da taimakon dakarun Faransa da Amurka su ne suka yi nasarar hallaka uku daga cikin maharan kafin daga bisanin suka karbe iko da Otel din mai suna Four Star Splandid wanda bakin kasashen ketere ke yawaita sauka a cikinsa.

‘Yan asalin kasar Canada 6 da ‘yan kasar Ukraine 3 da kuma Faransawa 3 na cikin wadanda aka tabbatar da mutuwarsu a harin na ranar jumma’ar da ta gabata.

Vall ya ce, harin na Ouagadougou na a matasayin tuni dangane da harin birnin Paris da kungiyar ISIS ta kai a watan Nuwamban bara tare da kashe mutane 130.

Tuni dai Al Qaeda ta bayyana Battar al-Ansari da Abu Muhammad al-Buqali da Ahmed al-Fulani al Ansari a matsayin ‘ya ‘yanta da suka kai harin na Burkina Faso.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.