Isa ga babban shafi
Burkina Faso-Mali

A na zaman makokin kwananki Uku a Burkina Faso

A fara zaman makokin kwananki Uku a yau Litinni a Burkina Faso sakamon harin ta'addanci da aka kai Ouagadougou wanda ya hallaka mutane 28. 

Friministan Burkina Faso Paul Kaba Thieba
Friministan Burkina Faso Paul Kaba Thieba AFP/AHMED OUOBA
Talla

Gwamnatin kasar na cigaba da bayyana takaicin ta da wannan hari al'amarin daya sa yanzu haka kasar da kuma Mali amincewa suyi aiki tare wajen musayar bayanna asiri da kuma aikin soji dan murkushe barazanar yan ta’addan da suka addabe su.

Firaministan Burkina Faso Paul Kaba Thieba da takwaran sa a Mali Modibo Keita ne suka sanar da hadin kan kwana guda bayan kazamin harin da aka kai Ouagadougou wanda ya hallaka mutane 28 daga kasashe 7.

Ba a dai yi bayani kan daukacin yarjejeniyar da shugabannin suka kulla ba, amma daga ciki akwai sintirin hadin gwuiwa tsakanin dakarun kasashen da kuma musayar bayanan asiri.

A bangare guda kuma, Shugaban Kasar Burkian Faso Marc Christian Kabore yace jami’an tsaro na farautar wadanda suka sace wasu ‘yan kasar Austria guda biyu da suke zama a cikin kasar tun shekarar 1972 inda suke kula da wani gidan shan magani.

A jawabin da ya yiwa al’ummar kasar ta kafar talabijin, shugaban ya bayyana wadanda aka sace a matsayin Kenneth da Jocelyn Elliot, inda ya bukaci al’ummar kasar da su taimaka wajen ganin an gano su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.