Isa ga babban shafi
Faransa-Burkina-Faso

Hollande ya yi bayanin farko akan harin Burkina Faso

Shugaban Faransa ya yi tsokaci a karon farko tun bayan aukuwar harin ta’addancin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 27 a birnin Wagadugu na kasar Burkina a makon da ya gabata 

Shugaban Faransa, François Hollande
Shugaban Faransa, François Hollande REUTERS/Mathieu Belanger
Talla

A jawabin farko na shugaban, Hollande ya ce burin ‘yan ta’adda shine ganin sun kara haifar da zaman zullumi  a kasar, inda suka bazu a gidajen abinci da otel otel, sai da sojojin Burkina da suka samu tallafin dakarun rundunar sojan musamman na Faransa wadanda na yabawa kwazon da suka nuna,wato  wajen kubutar da mutane 120 din da yan ta’addan suka yi garkuwa dasu.

Shugaba Hollande ya ci gaba da cewa akwai mutanen da suka jikkata, sai dai ya ce a halin yanzu bashi da cikakken sakamakon yawan su, inda yanzu haka dai ana ci gaba da tantance sauran mutanen da abin ya shafa acewar Hollande.Sojojin Faransa sun taimakawa sojojin Burkina wajen kubutar da wadanda mayakan suka yi garkuwa dasu.

Daga karshe shugaba Hollande ya bayyana harin a matsayin na kaskanci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.