China
China za ta kori wata ‘yar jaridar Faransa
China zata kori wata yar jarida, Bafaransa bayan kasar ta ki amincewa ta sabunta takardunta na aikin jarida saboda wani labari da ta rubuta da bai wa mahukuntan kasar dadi ba.
Wallafawa ranar:
Talla
Ursula Gauthier na aiko da rahoto ne daga Beijing a wata mujallar Faransa, kuma ma’aikatar harakokin wajen China tace sai ta rubuta takardar neman gafara kafin a sabunta takardunta na ci gaba da aikin jarida a kasar.
Kungiyoyin da dama masu kare hakkin ‘Yan jaridu sun yi allawadai da matakin.
A ranar 31 ga watan Disemba yar jaridar zata bar China.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu