Afrika ta Tsakiya
An kashe wata ‘Yar Jaridar Faransa a Afrika ta tsakiya
An kashe wata ‘Yar Jaridar kasar Faransa mai daukar hoto a wani harin kwantar bauna yayin da ta ke gudanar da aikinta a kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya mai fama da rikicin addini. Fadar shugaban kasar Faransa tace wasu dakarun wanzar da zaman lafiya ne suka tsinci gawar Camille Lepage a cikin wata mota da wasu mayakan Anti Balaka ke ciki a yankin Bour da ke Yammacin kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
Kisan Lepage na zuwa ne duka watanni shida da aka kashe wani dan jarida a kasar Mali.
Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah waddai da kisan ‘Yar Jaridar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu