Isa ga babban shafi
Faransa

An samu raguwar ‘yancin gudanar da aikin Jarida a duniya

Kungiyar da ke sa ido kan ayyukan kafofin yada labarai a duniya da ake kira Reporters Without Borders ta ce an samu raguwar ‘yancin gudanar da ayyukan jarida a duniya baki daya saobda ayyukan ta’addanci na Mayakan IS a Gabas ta tsakiya da Boko Haram na Najeriya.

Jaridun kasar Faransa
Jaridun kasar Faransa
Talla

Shugaban da ke jagorantar Kungiyar a Faransa Christophe Deloire ya danganta matsalolin da suka haifar da haka da suka hada da yake-yake da tashin hankali da kuma matakan da kungiyoyi da gwamnatoci ke dauka.

Rahotan kungiyar ya ce an samu laifuka 3,719 wajen hana ‘yan jaridu gudanar da ayyukansu a kasashe 180 a shekarar da ta gabata, wanda wannan adadin ya haura da Karin kashi 8 a shekarar 2013.

Rahotan kungiyar ya ce kungiyoyi irin su ISIS a Iraqi da Syria da ayyukan Boko Haram a Najeriya da Kamaru da kuma kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasashen Italiya da Amurka ta kudu sun aikata laifuka wajen afkawa manema labarai.

Rahoton ya ce rewacin Afrika da Gabas tsakiya nan ne yankuna mafi hatsari ga aikin jarida a duniya.

Kazalika, rahoton ya ce matsalar ‘yancin ‘Yan Jarida ta fi kamari a kasashen China da Syria da Korea ta arewa da Iran cikin kasahe 180 da kungiyar ta gudanar da bincike.

Rahoton ya bayyana kasashe irinsu Finland da Norway da Denmark da Holland da Sweden da Jamaica da Canada a matsayin kasashen da ake mutunta ‘yancin ‘Yan jarida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.