Isa ga babban shafi
Argentina

Shugabar Argentina ta yi ban-kwana da masoyanta

Shugabar Argentina mai barin gado, Christina Fernadez de Kirchner ta gabatar da jawabin ban-kwana ga dubban magoya bayanta a wani dandali da ke babban birnin Buenos Aires.

Shugabar Argentina mai barin gado, Cristina Kirchner.
Shugabar Argentina mai barin gado, Cristina Kirchner. Fuente: Reuters.
Talla

A jawabinta, shugabar ta yabi irin rawar da gwamnatinta ta taka a cikin shekaru takwas wajen kawo ci gaba a kasar yayin da ta caccaki gwamnati mai jiran gado.

Shugabar ta bukaci al-ummar kasar da su gudanar da zanga zanga a kan titunan kasar da zaran sun ga cewa sabuwar gwamnatin ta yaudare su.

Ana sa ran wani lokaci a yau Alhamis, za a rantsar da sabon shugaban kasar Mauricio Marci yayin da Christina ta sanar cewa ba za ta halarci bikin rantsar da shi ba, lamarin da ya sa wasu suka caccake ta.

Sabuwar gwamnatin dai za ta fuskanci kalubale musamman ta fuskar tattalin arzikin kasar, inda a yanzu haka aka samu karin kashi 25 cikin 100 na tashin farashin kayayyaki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.