Isa ga babban shafi
Argentina

Kirchner ta Argentina za ta bar baya da kura

Shugabar kasar Argentina Cristina Kirchner za ta bar baya da kura, yayin da za a gudanar da zaben kasar a ranar lahadi mai zuwa, inda za a zabi magajinta.

Shugabar kasar Argentina Cristina Kirchner.
Shugabar kasar Argentina Cristina Kirchner. REUTERS/Enrique Marcarian
Talla

Christina Kirchner wadda ta gaji mulki bayan rasuwar mijinta kuma tsohon shugaba kasar Nestor Kirchner, ta shafe shekaru da dama tana jan ragamar siyar Argentina, yayin da lokacin saukarta daga karagar mulki ya cika, lamarin da zai sa a gudanar da zabe domin samun wanda zai maye gurbinta kuma ana ganin hakan zai haifar da rarrabuwan kawunan jama’a a kasar.

Kirchner da majinta sun taka rawar gani wajan ceto tattalin arzikin Argentina bayan ya gamu da matsala tun a shekara ta 2001.

Duk da caccakar da wasu ke yi mata, Kirchner ta yi kokarin farfado da tattalin arzikin kasar kuma ta tafiyar da kasar cikin mayar da martini da suka ga masu yi mata adawa da suka hada da Kasar Birtaniya wadda ta yi takun saka da Argentina sakamakon rikicin tsibirin Falkland.

To sai dai wasu daga cikin ‘yan kasar sun yi tir da gwamantinta kamar Monica Gurfinkel, mai shekaru 48 wadda ta bayyana Kirchner a matsayin babbar makaryaciya kuma ta ce, ta tsane ta.

Shi kuwa Juan Bertone, mai shekaru 32 kuma ma’aikacin banki cewa ya yi, Kirchner ita inganta rayuwar al-ummar kasar a kuma dole ne a nuna mata kauna.

A shekara ta 2007 ne, Christina Kirchner mai shekaru 62 ta dare kan kujerar shugabancin kasar, inda ta yi alkawarin ci gaba da aikin da mijinta kuma tsohon shugaban kasar ya fara, yayin da ta yi tazarce a shekara ta 2011 bayan an sake zabenta, kuma yanzu ba ta da damar sake tsayawa takara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.