Isa ga babban shafi
Argentina

Macri ya lashe zaben Argentina

Dan Takaran Jam’iyar adawar kasar Argentina Mauricio Macri ya lashe zaben shugaban kasar zagaye na biyu da aka gudanar a karshen mako abin da ya kawo karshen sama da shekaru 10 da shugaba Cristina Kirchner da mijinta suka kwashe akan karagar mulki a kasar.

Sabon shugaban Argentina Mauricio Macri
Sabon shugaban Argentina Mauricio Macri REUTERS/Enrique Marcarian
Talla

Macri wanda Magajin Garin Buenos Aires ne kuma tsohon shugaban kungiyar kwallon kafar Boca Juniors da ta lashe kofuna 17 a karkashin jagorancinsa, ya yi alkawarin kawo sauyi kan yadda ake tafiyar da kasar musamman fannin tattalin arzikin kasa.

Macri ya lashe zaben ne zagaye na biyu da sama da kashi 51 na kuri’un da aka kada, yayin da abokin hamayyarsa Scioli ya samu kuri’u kashi 48.2 daga cikin kashi 95 na kuri’un da aka kidaya.

Tuni kuma Daniel Scioli ya amince da sakamkon zaben tare da amsa shan kaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.