Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande zai gana da shugabannin duniya kan IS

A ci gaba da kokarin ganin an dauki matakin bai-daya don murkushe kungiyar IS, shugaban kasar Faransa Francois Hollande zai gana da shugabannin kasashen duniya da dama a cikin wannan mako.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande REUTERS/Michel Euler/Pool
Talla

Wannan ganawar dai ta biyo bayan kazamin harin da aka kai birnin Paris wanda ya hallaka mutane 129 inda kuma kungiyar IS tace ita ta kai harin da kasashen duniya suka la’anta.

Shugaba Francois Hollande ya bukaci sauya kundin tsarin mulkin Faransa domin sanya wasu sabbin dokoki da zasu bayar da damar yaki da yan ta’adda da kuma korar bakin da suka fito daga wata kasa da ke zama barazana ga zaman lafiya ga Faransa.

Cikin shugabanin da Hollande zai gana da su sun hada da Barack Obama na Amurka da Vladimir Putin na Rasha da David Cameron na Birtaniya da kuma Angela Merkel ta Jamus.

Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy a ziyarar jaje da ya kai wa Hollande ya bukaci hadin kai da Putin don murkuse IS da ta dauki alhakin kai harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.