Kasashen duniya sun yi tir da harin Bamako
Kungiyar ta’adda mai alaka da Alqa’ida da ake kira Al Mourabitoun, ta yi ikirarin kai wannan harin da da aka kai a Hotel Radisson da ke birnin Bamako.
Wallafawa ranar:
Yayin da kasashen duniya suka yi tir da kuma Allah Wadai da hakan, shugaban Amurka Barack Obama, wanda yanzu haka ke halartar taron shugabannin kasashen yankin Asiya da Pasifik, ya yi kakkausar suka a game da wannan hari da aka kai a Bamako.
Shi ma dai bababban magatakarda na MDD Ban Ki-moon, ya ce ya damu matukar a game da halin da kasar ta Mali ta fada a daidai lokacin da kasashen duniya ke kokarin taimaka wa Mali domin komawa kan turbar dimokuradiyya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu