Isa ga babban shafi
Duniya

Munanan hare haren ta’addanci a duniya

Jerin hare haren da ‘Yan ta’adda suka kai a Paris a ranar Juma’a na daya daga cikin munanan hare haren da aka kai a kasashen duniya musamman tun bayan ruguza tagwayen benaye da ke birnin New York na Amurka a shekara ta 2001.

Kasashen Duniya sun taya Faransa jimamin hare haren da aka kai a birnin Paris
Kasashen Duniya sun taya Faransa jimamin hare haren da aka kai a birnin Paris Anne Bernas/RFI
Talla

A ranar 13 ga wannan watan ne, wasu jerin hare haren da IS ta yi ikirarin kai wa a Faransa, suka hallaka mutane akalla 129. A ranar 12 ga watan ne kuma, wani harin kungiyar ta IS a birnin Beirut na Lebanon ya yi sanadiyar mutuwar mutane 44.

A ranar 31 ga watan Oktoban daya gabata ne, jirgin Fasinjan Rasha ya yi hatsari a yankin Sinai na Masar tare da kashe mutane 224 inda Mayakan IS suka yi ikirarin kakkabo jirgin, kamar yadda Amurka da Birtaniya ke zargin Bam ne ya tarwatsa jirgin.

A ranar 10 kuwa ga watan na Oktoba, mutane 102 suka rasu a Turkiyya, inda kuma a ranar 26 ga watan Yunin daya gabata, wani dan bindiga ya hallaka yan yawon bude ido 38 a Tunisiya.

A ranar 2 ga watan Afrilun wannan shekarar Al- Shebab da ke alaka da Al-Qaeda ta kashe mutane 144 a jami’ar Garissa ta Kenya.

A ranakun 7 zuwa 9 a watan Janairun daya gabata, wasu ‘yan bindiga suka kashe mutane 12 a ofishin mujallar Charlie Hebdo ta Faransa.

A ranakun 21 zuwa 29 a shekara ta 2013, Al-Shebab ta kashe mutane 67 a shagunan Westgate na Kenya.

A ranakun 26 zuwa 29 a shekara ta 2008 a India, ‘yan bindiga suka kashe mutane 166.

A ranar 7 ga watan Yulin shekara ta 2005 a Birtaniya, wasu jerin hare haren kunar bakin wake sun kashe mutane 56.

A ranar 11 ga watan Maris na 2004 a Spain, bama bamai suka kashe mutane 191 a birnin Madrid

A ranar 12 ga watan Octoban 2002 a Indonesia, wasu hare hare suka hakkala mutane 202 yayin da ranar 11 ga watan Satumban 2001 a Amurka, kimamnin mutane 3,000 suka mutu sakamokn kazamin farmakin da Al-Qaeda ta ce, ita ta kaddamar a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.