Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka nada yakinin kashe jihadi John

Sojojin Amurka sun bayyana cewa suna da kwarin gwiwar kashe jihadi John a hare haren saman da suka kaddamar a Syria, yayin da Birtaniya ta ce harin na Amurka wani mataki ne na kare kanta.

Jihadi John da ake tunanin an kashe shi a hare haren da Amurka ta kai Syria.
Jihadi John da ake tunanin an kashe shi a hare haren da Amurka ta kai Syria. REUTERS/SITE Intel Group/Handout via Reuters/Files
Talla

A cikin wata sanarwa da firaministan Birtaniyya David Cameron ya fitar, ya bayyana cewa farmakin na ranar Ahamis din da ta gabata kan jihadi John wanda ya saba fito wa a faya-fayen bidiyo da ke nuna yadda masu da’awar jihadi ke kashe ‘yan kasashen yamma da suka yi garkuwa da su, hadin gwiwa ne tsakanin Amurka da Birtaniyya.

Cameron ya kara da cewa, matukar aka tabbatar da mutuwar Jihadi john, to lallai hakan zai bakanta ran mayakan kungiyar IS.

A nashi bangaren, sakatern harkokin wajen Amurka, John Kerry da ke ziyara a Tunisiya, ya ce kwanaki kalilan ya rage a kawo karshen kungiyar ta IS, yayin da mayakan kurdawan Iraqi su ma suka ce, kungiyar ta sha fatattaka a birnin Sinjar da ke yankin arewacin kasar.

Jihadi John, masanin kwamfuta a birnin Landan, an haife shi ne a kasar Kuwait amma iyayesa ‘yan asalin Iraqi ne kuma a shekara ta 1993 ne suka koma Birtaniyya da zama bayan sun fitar da ran samun takardun shaidan zama dan kasa a Kuwait.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.