Isa ga babban shafi
MDD

Gudun Hijira: Ana haihuwar ‘ya’yan da ba su da kasa

Majalisar Dinkin Duniya tace a cikin ko wane mintuna 10 ana haihuwar yaron da bashi da kasar da zai ce tasa ce, sakamakon tahsin hankali, wanda hakan ke matukar illa ga rayuwarsa.

'Yan Gudun Hijirar Syria da Iraqi na ci gaba da kwarara zuwa kasashen Turai
'Yan Gudun Hijirar Syria da Iraqi na ci gaba da kwarara zuwa kasashen Turai Relief & Reconciliation for Syria
Talla

Shugaban hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutheres ne yafadi haka, yana mai cewa matsalar na yiwa yara illar da zai kasance da su har iya rayuwarsu, ganin irin kyamar da za su fuskanta daga sauran al’umma.

Gutheres ya ce irin wadannan yara kan fuskanci matsaloli irinsu rashin samun ilimi da rashin kula da lafiyarsu da kuma samun ayyukan yi.

Jami’in ya ce a cikin kasashe 20 da yanzu haka suke dauke da yan gudun hijira akalla yara 70,000 ake haifa da ba su da kasarsu ta kansu a duk shekara, wanda hakan ke nuna ana haihuwar yaro guda ko wane mintina 10.

Rahotan da ake shirin kaddamar da shi a yau laraba a Cibiyar Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci tantance irin wadannan yara a kasashe 30 don samun kula da lafiyar su, da wasu kasashe 20 domin yi mu su rigakafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.