Isa ga babban shafi
SYRIA-MDD

“Ya kamata Turai ta yi koyi da Turkiya akan ‘Yan gudun hijira”

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar Duniya ta bukaci kasashen yammaci su bi sahun Turkiya wajen bude iyakokinsu domin karban ‘yan gudun hijira da ke ci gujewa rikicin Syria. Hukumar tace akalla mutane miliyan 60 ne ke gudun hijira a sassa daban-daban da ake fama da yake-yake.

Sansanin 'Yan gudun Hijirar syria a Lebanon
Sansanin 'Yan gudun Hijirar syria a Lebanon Reuters/Jamal Saidi
Talla

A lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a birnin Istanbul na kasar Turkiya, Kwamishina a hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce akwai bukatar kasashen yammaci su taimaka wajen karban ‘yan gudun hijira, lura da cewa a yanzu haka akwai kusan ‘yan gudun hijira Syria miliyan 2 da Turkiya ke dawainiya da su.

Antonio ya ce yana da muhimmaci Tarayyar Turai da kasashen da ke yankin Gulf su bude iyakokinsu domin karban ‘yan gudun hijira musamma na Syria.

Antonio wanda ke yabawa namijin kokarin Turkiya, ya ce nauyin ya yi wa kasar yawa akwai bukatar a agaji daga wasu kasashen.

Majalisar Dinkin Duniya tace, a shekarar da ta gabata akalla mutane miliyan 60 ne rikice-rikice, da yaki, ya tursasawa gujewa kasahensu. Kuma Yawancinsu yara ne kanana.

Antonio Guterres dai na gani cewa rashin kwanciyar hankali na taka muhimmiyar rawa wajen karuwar bakin haure da ke kokarin ketara teku a kullum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.