Isa ga babban shafi
SYRIA

ISIL na kara samun nasara a Syria

Da alama Kungiyar ISIL na cigaba da samun nasara kwace ikon manyan birane a Syria, inda a yanzu haka mayakan sun kafa tutarsu a birnin Hasakeh bayan fatataka dakarun tsaro daga yankin.Wannan dai na zuwa ne, bayan gamayar sojojin kawance karkashin Jagoranci Amurka sunyi nasara tarwatsa wani rumbu da mayakan ke ajiyan bama-bamai.

Mayakan IS da ke da'awar Jihadi a Syria
Mayakan IS da ke da'awar Jihadi a Syria REUTERS/Rodi Said
Talla

Duk da irin hare-haren sama da gamayar dakarun sojin Amurka ke kaiwa akan mayakan na ISIL, tsahon watanin 9 yanzu, mayakan na cigaba da samun nasara musamma a yan satutuka na a Syria da Iraqi, bayan kame ikon Palmyra da Ramadi da kuma lardin Anbar.

Bayan kame ikon Hasakeh a yanzu, mayakan sun kara fadada yakin nasu da nufin cigaba da kame manyan garuruwan yankuna Syria da Iraqi, kamar yadda Rami Abdel Rahman Jam’in kungiyar da ke sa’ido akan harkokin Syria ya tabbatar

Rami ya ce a halin da ake cikin yanzu, Mayakan ISIL sun kwace duka sansani sojin da ke arewa maso gabashin Syria, tare da tarwatsa gidan yari da ke yankin da tashar samar da wutan lantarki, inda sukayi amfani da wasu ‘yan kunar bakin wake 6 wajen tarwatsa jami’an tsaro

Kwace ikon birnin Hasakeh ba karamin kara tabarbare lamura bane a Syria, kasancewa shine birni na 2 mafi muhimmaci daya sake faduwa a hannu mayakan bayan yankin Raqa da Idlib.

Kasahsen Iran da Iraqi sun tura duban dakarun sojojin da mayakan sa kai zuwa Syria domin taimaka musu wajen kare babban birni kasar na Damascus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.