Isa ga babban shafi
Kyautar Nobel

Masana kiwon lafiya uku sun lashe kyautar Nobel

Masana kiwon lafiya uku ne a yau litinin aka sanar a matsayin wadanda suka  lashe Kyautar Nobel ta bana a fannin lafiya, bayan nasara da suka samu wajen samar da magungunan cuttutukan zazzabin cizon sauro da tsutsar ciki.

William Campbell, Satoshi Omura da Tu Youyou.
William Campbell, Satoshi Omura da Tu Youyou. AFP PHOTO / JONATHAN NACKSTRAND
Talla

Mutanen uku da suka kun shi Tu Youyou ta Chana da William Campbell na kasar Ireland da kuma Satoshi Omura na kasar Japan su suka lashe kyautar Nobel a bana, sakamakon jajircewarsu na gano maganin da zai yaki cutar zazzabin cizon sauro ko malariya da cutar nan ta tsutsar ciki dake hadassa asarar rayuka da dama a duk shekara musanman ma a kasashen Afrika.

Acewar kwamitin dake kula da kyautar ta Nobel ta yabawa wadanan masanan kiwon lafiya a kokarin su na taimakawa rayuwar al’umma da makami na yakar cututukan nan biyu dake barazana ga lafiyar dan adam.

Tu Youyou mai shekaru tamanin da hudu ita ta gano maganin zazzabin cizon sauron mai suna Artemisin kuma ta karbi rabin kyautar a yayin da Avermectin ya kasance kokarin Omura da Campbell maganin dake iya yakar duk wata kwayar cuta dake haddasa tsutsar ciki.

Masanan kiwon lafiyar ukun zasu kuma raba kudi dala dubu dari tara da hamsin a tsakaninsu a matsayin tukiyicin dake zuwa da kyautar ta Nobel.

Alkaluman hukumar lafiya ta duniya WHO na cewa mutane sama da miliyan dari daya da casa’in ne Cutar Malariya ta kama a shekara ta 2013 yayin da mutune sama da dubu dari biyar suka mutu yawancinsu yara ne a kasashen Africa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.