Isa ga babban shafi
Nobel

Shugaban kyautar Nobel ya koma matsayin Mamba

An yi bankwana da Shugaban kwamitin bada kyautar Nobel ta zaman lafiya Thorbjørn Jagland, inda aka mayar da shi a matsayin Mamban, al’amarin da ya kasance irinsa na farko da wani shugaban Kwamitin ya fuskanta, tun bayan kafa shi kimanin shekaru 100 da suka gabata.

Malala Yousafzai ta Pakistan Kailash Satyarthi na India da suka lashe Kyautar Nobel a 2014.
Malala Yousafzai ta Pakistan Kailash Satyarthi na India da suka lashe Kyautar Nobel a 2014. REUTERS/Cornelius Poppe/NTB Scanpix/Pool
Talla

Bayan da aka zabe shi kan karagar shugabancin kwamitin na bayar da kyautar Nobel a 2009, kwamitin ya shiga shan suka sakamakon kyautar da ya bai wa shugaban kasar Amurka Barack Obama, da wani mai fada a jin kasar China Liu Xiaobo da kuma kungiyar Tarayyar Turai.

Yanzu haka za a maye gurbinsa ne da mataimakiyarsa.

A tarihi dai ba a taba samun wani shugaban Kwamitin bada kyautar ta Nobel da ya yi fatan ganin an sake zabensa a kan mukamin ba kamar yadda M. Jagland, ya bukata.

Uwar gida Kullman Five dai taki ta yi wani furuci dangane da dalilan da suka hana sake zaben magabacinta kan mukamin duk da cewa ya fito fili ya bayyana bukatarsa ta son yi masa hakan.

A lokacin da ta ke bayani a gaban manema labarai Kullman Five ta ce, a karkashin doka ba ta da ikon yin wani furuci ko bayyana abubuwan da zaman taron kwamitin na nobel mai mambobi 5 ya tattauna a kai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.