Isa ga babban shafi
Syria-MDD

Tawaggar masu lalata makamai masu guba a Siriya ta sami kyautar Nobel

A yau Jumu’a Kungiyar dake kula da lalata Makamai masu Guban kasar Siriya ta samu lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel, akan kokarin ta na tabbatar da ganin an hana amfani da Makami mai Guba a Duniya.Wannan dai ya faru ne sakamakon zabe mai cike da ban mamaki, da aka yiwa wannan Kungiyar bayan da kwamitin dake shirya bada kyautar Nobel ta zaman lafiya a Duniya ya goyi bayan wannan kungiya da ayukan da take.Yakin dake faruwa a kasar Siriya tsakanin gwamnati da ‘yan tawaye, da ya haddasa sake amfani da Makami mai Guba a kasar ne, ya sake zafafa kaifin aikin wannan Kungiyar da kuma kara bada fifiko ga ganin an kai karshen amfani da Makami mai Guba a Duniya baki daya.Yanzu haka dai akwai ayarin kwararru masu aikin lalata Makami mai Guban su 30, da ke a kasar Syria da kuma jami’an Majalisar Dinkin Duniya da suka fara lalata Makamai masu Guban kasar.Itama dai Yarinyar nan mai Suna Malala Yusuf-Zai, mai fafutukar samar da Ilimi ga yara Mata, wadda ta tsallake rijiya da baya, bayan da ‘yan kungiyar Taliban suka harbe ta, da kuma wani Likita a kasar Congo na daga cikin wadanda suka samu wannan kyautar.Shugaban kasar Faransa Francious Hollande ya yaba da ayyukan kwamitin bada kyautar Nobel din, saboda karrama kungiyar kwararrun ta lalata Makamai masu Guba a Duniya.  

Tawaggar masu sa ido kan makamai a Siriya, yayin da suke gudanar da aikin su
Tawaggar masu sa ido kan makamai a Siriya, yayin da suke gudanar da aikin su REUTERS/Mohamed Abdullah/Files
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.