Isa ga babban shafi
Saudi

Saudiyya Ta Kare Kanta daga Zargin mutuwar Alhazai

Kasar Saudiyya ta kare kanta daga zargi da wasu keyi mata cewa sakacin ta ya janyo mutuwar mutane 769 a wajen jifan shaidan na farko ranar Alhamis data gabata. 

Ministan Waje na kasar Saudiyya Adel Al-Jubeir tare da Ministan waje na Rasha Sergei Lavrov
Ministan Waje na kasar Saudiyya Adel Al-Jubeir tare da Ministan waje na Rasha Sergei Lavrov REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Ministan waje na kasar Saudiyya Adel Al-Jubeir ya fadi cewa bai dace ba kasar Iran ta maida wannan tsautsayi harkan siyasa.

A cewar Ministan, Saudiyya ta dauki matakai da suka dace domin nasarar aikin hajjin na bana.

A yanzu haka dai Hukumomin Saudiyyan na cigaba da gudanar da cikakken binciken musabbabin wannan turmutsitsi.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.