Isa ga babban shafi
Saudi

Mahajjata sun ci gaba da jifan Shaidan a Saudiya

A yau juma’a mahajjata sun ci gaba da aikin jifar shedan bayan hatsarin da ya faru har aka samu asarar rayukan mutane sama da 700 lokacin da mahajjata ke kokarin isa Mina.

Duk da mutuwar Mahajjata sama da 700 a jiya alhamis, an ci gaba da aikin jifan shaidan a yau.
Duk da mutuwar Mahajjata sama da 700 a jiya alhamis, an ci gaba da aikin jifan shaidan a yau. REUTERS/Ahmad Masood
Talla

Rahotanni sun ce yawan mutanen da suka fito akan titunan da ke isa Jamarat inda ake aikin jifar shedan a safiyar yau ya sha bamban da wanda aka gani a jiya alhamis.

Kawo yanzu dai hukumomin Saudiyya ba su fitar da jerin sunayen kasashen da mamatan suka fito ba, to sai dai daga yammacin Afirka akwai mahajjata daga Najeriya, Nijar, Cote d’ivoire Mali da kuma Senegal da suka rasu.

A nata banagren kasar Iran ta fitar da sabbin alkalumma a yau dangane da yawan Yan Kasar da suka rasu a turmutsitsin, inda ta ce Mahajjatanta 131 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 60 suka samu raunuka.

Sarki Salman na Saudiya ya bukaci a sake nazarin tsare tsarern gudanar da aikin Hajji yayin da Shugaban Kwamitin aikin Hajji Yarima Muhammad bin Nayyef ya kaddamar da bincike game da aukuwar turmutsitsin.

A bangare guda, Ministan lafiya na Saudiya, Khaled Al-Falih ya dore laifin aukuwar turmutsitsin kan Mahajjata, inda ya ce da Mahajjatan sun bi ka’idojin da aka gindaya, da hadarin bai faru ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.