Mutane sama da 700 sun rasu a tirmutsitsin aikin Hajji.
Sama da Mutane 700 sun rasa rayukansu sakamakon tirmutsutsun da ya auku a lokacin jifan Shaidan a Saudiyya a yayin da wasu da dama suka jikatta kamar yadda hukumomin Kasar suka sanar a yau Alhamis.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
To sai dai Kawo yanzu ba’a sanar da musabbabin tirmutsustsun ba a hukumance yayin da jirage masu saukan ungulu ke ci gaba da shawagi a sararin samaniyar inda abin ya faru don fadada bincike.
Tuni dai Jami'an bada agajin gaggawa sama da dubu 4 suka isa wurin domin taimakawa wadanda suka jikkata kuma kimanin Motocin daukan marasa lafiya 220 aka tura wurin.
A ranar 11 ga wannan watan na satumba ne wata kugiyar daukan kayayyakin gine-gine ta rikito cikin masallacin Ka’abah inda ta yi sanadiyar mutuwar maniyatta hajji sama da 100.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu